Zamfara: Yari Ya Yi Amai Ya Lashe

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Alhaji Abdulaziz Yari, ya ba da umarnin gaggawa na janye kara uku da ya shigar da shugabancin jam’iyyar APC.

An ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan sulhun da aka yi tsakanin ɓangarorin APC biyu na Zamfara masu adawa da juna.

Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sasanta tsagin Gwamna Bello Matawalle da tsagin tsohon gwamna Yari da Sanata Kabiru Marafa a kwanakin baya.

Wannan sulhu da aka samu tsakanin ɓangarorin ya bude sabon shafi na harkokin siyasar jam’iyyar APC mai mulki reshen jihar Zamfara.

Kafin samun masalaha a tsakanin, saɓanin jiga-jigan siyasa a Zamfara ya haddasa darewar jam’iyyar APC har aka samu shugabanni biyu. Duk wani yunkuri na kawo karshen sabanin ɗake tsakani da kwamitin rikon kwarya karkashin gwamna Mai Mala Buni, ya yi a wancan lokacin bai haifar da ɗa mai ido ba.

Wata majiya ta ce sanarwan janye karar ta fito ne daga hannun Sanata Marafa jim kaɗan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a Garba Nadama Hall, Gusau, ranar Laraba.

Marafa ya faɗa wa dandazon mutane cewa zasu janye karan ne domin tabbatar da sulhun da kuma baiwa gwamna Matawalle goyon bayan da ya dace wajen shawo kan matsalar tsaro.

“Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta dunƙule wuri ɗaya karkashin shugabanci ɗaya kuma dukkan ƴaƴan jam’iyya na aiki tare cikin zaman lafiya da cigaban jiha.”

Labarai Makamanta