Zamfara: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Yi Wa Matawalle Tawaye

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya daga jihar su Shida waɗanda suka koma jam’iyyar APC tare da gwamna Matawalle sun yi amai sun lashe.

‘Yan majalisar wakilan sun sake komawa jam’iyyar PDP kuma sun karɓi tikitin takara a babban zaɓen 2023 ba tare da hamayya ba.

‘Yan majalisar sun sake komawa PDP ne sakamakon yarjejeniyar da aka yi yayin sulhun gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon gwamna Abdul-Aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa.

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC ta hana yan majalisun damar siyan Fom ɗin tsayawa takara a zaɓen 2023 saboda ta riga da ta ba wasu sabbi kujerun su.

‘Yan Majalisar da suka koma PDP ɗin sun haɗa da, Honorabul Ahmad Maipalace na mazaɓar Gusau/Tsafe, Honorabul Bello Hasan na mazaɓar Shinkafi/Zurmi da Honorabul Sulaiman Gummi na mazaɓar Gummi/Bukkuyum.

Sauran su ne; Honorabul Sani Umar na mazaɓar Kaura-Namoda/Birnin Magaji, Honorabul Shehu Ahmad na mazaɓar Maru/Bungudu, da kuma Honorabul Ahmad Muhammed mai wakiltar mazaɓar Bakura/Maradun a majalisar tarayya.

Labarai Makamanta