Zamfara: ‘Yan Majalisa Sun Amince Da Tsige Mataimakin Gwamna

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar na bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar ta jefa ƙuria’r amincewa da tsige Mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau daga kan muƙaminsa da gagarumin rinjaye.

Yayin wani zama a jiya Alhamis, ‘yan majalisa 18 cikin 22 ne suka amince da ɗaukar matakin yayin da ɗaya tak ya ki amincewa.

Haka nan, ‘yan majalisar sun nemi Alƙalin Alƙalai na Zamfara Mai Shari’a Kulu Aliyu ya kafa Kwamitin da zai binciki Mahdi bisa zargin saɓa sashe na 190 da 193 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Dangantaka tsakanin mataimakin gwamnan da uban gidansa Gwamna Bello Muhammad Matawalle ta yi tsami tun lokacin da gwamnan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a bara amma Mahdi ya ci gaba da zama a PDP.

Labarai Makamanta