Zamfara: ‘Yan Majalisa Na Shirin Tsige Mataimakin Gwamna

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan Majalisar dokokin Jihar sun fara shirye-shiryen tumbuke mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Gusau, daga mukamin shi.

Hakan ya biyo bayan wata takarda ta kora ga mataimakin gwamnan wanda aka gabatar ga kakakin majalisar dokokin Jihar.

Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar, Musa Bawa, ya gabatar da takardar ga kakakin majalisar, Nasiru Mu’azu a ranar Juma’a a farfajiyar majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar.

An tattaro bayanai akan yadda majalisar ta zargi mataimakin gwamnan da yin karantsaye ga kundin tsarin mulki, tozarta mukaminsa da kuma satar kudade.

A cewar Bawa yayin gabatar da takardun a wani kwarya-kwaryan taro da suka yi a ofishin kakakin: “Ina gabatar da wannan takardar ga kakakin majalisa, Nasiru Mua’zu Magarya akan tumbuke mataimakin gwamnan Jihar Zamfara.”

Lokacin da Mu’azu ya amshi takardun ya yi alkawarin duba takardun inda yace zai dauki mataki daidai da abinda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

“Ka zo nan ofishi na, mataimakin kakakin majalisa kuma shugaban kwamitin asusun gwamnati, kuma ka gabatar min da takardun cire mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Gusau. “Na amsa kuma ina mai tabbatar muku da cewa zan yi aiki bisa yadda kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka gyara a 1999 ya tanadar.”

Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Mahadi Gusau ya ci gaba da nuna rashin yardarsa akan abubuwa da dama tun bayan gwamnan ya sauya jam’iyya.

Matawalle ya zama gwamna a karkashin jam’iyyar PDP kuma tun watan Yunin shekarar da ta gabata ya sanar da komawarsa APC. Yayin da kowa ya yi tunanin mataimakinsa zai bi sahun sa, Gusau ya bayyana a taron PDP inda ya ce yana nan a jam’iyyar babu gudu babu ja da baya.

Labarai Makamanta