Zamfara: ‘Yan Daba Sun Tarwatsa Taron PDP

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu gungun matasa dauke da makamai da ake kyautata zaton ‘yan daba ne sun kai hari filin da jam’iyyar PDP take gudanar da taro a birnin na Gusau.

Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa tun da fari an so a gudanar da taro a Zaitun Oil mill, da ke bayan hukumar alhazai amma aka sauya zuwa Command Guest House da ke Gusau.

Rahotanni sun ce ‘yan dabar siyasa sun yi wa wurin dirar-mikiya da sanyin safiyar ranar Litinin inda suka lalata kayayyakin zabe da fom-fom da motocin ‘yan jam’iyyar PDP da kuma kujeru sannan suka cinna wuta kan rumfunan da aka kafa.

Hotunan da aka rika watsa a shafukan intanet sun nuna yadda wurin ya kama da wuta bayan an yi kaca-kaca da shi.

Rahotanni sun ambato Umar Aminu, wani hadimin mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, yana cewa babu wanda ya isa ya yi musu barazanar da za ta kai su fasa gudanar da taron.

An soma zaman doya-da-manja tsakanin Gwamna Mohammed Matawalle da mataimakinsa tun bayan gwamnan, wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Labarai Makamanta