Zamfara: Uwargidan Gwamna Ta Bukaci A Sa Jihar Cikin Addu’a


Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Aisha Bello Matawalle ta yi ƙira ga Musulmin jihar da su gudanar da addu’o’i na musamman a yayin Sallar Eidi don neman taimakon Allah wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar jihar da ƙasa baki daya.

Wannan na cikin wani jawabi da Sakatariyar watsa labaran matar gwamnan ta fitar, Zainab Shu’aibu Abdullahi a safiyar Talata.

A cewar uwargidan gwamnan, “Ranar Babbar Sallah wadda ta yi daidai da ranar Ibadar ƙarshe ta aikin hajjin bana a ƙasa mai tsarki dama ce ga musulmai don yin amfani da wannan lokacin wajen neman taimakon Allah don samar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.”

Hajiya A’isha Matawalle ta taya ɗaukacin musulmin jihar Zamfara murnar ganin watan Babbar Sallah.

“Yayin da muke bikin wannan Sallah, bai kamata mu manta da jihar mu da ƙasar mu ba a cikin addu’o’in mu.

“Ya kamata mu yi koyi da kyawawan halayen taimaka wa masu ƙaramin karfi da marasa galihu kamar yadda addinin Islama ya umarta”

“Mata su ma su himmatu wajen kula da gidaje da iyalun su a lokacin wannan buki domin gudanar da shi lami lafiya”.

Ta ƙara da cewa, “yana da matuƙar muhimmanci mata ku mara wannan gwamnati mai ci yanzu ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammad Bello Matawalle baya don samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar, “, in ji Uwargidan Shugaban kasar.

Labarai Makamanta