Zamfara: Umarnin Mallakar Bindiga Ya Haifar Da Cece-Kuce

Shawarar da gwamnatin jihar Zamfara ta yanke ta bai wa dukkan mazauna Jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ta jawo ce-ce–ku-ce.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da kuma hakan zai ba mutane musamman manoma damar kare kawunansu a lokaci da suke gudanar da ayyukansu.

“Hare-haren ta’addanci sun kasance abin damuwa ga jama’a da gwamnatin jiha. Don haka ne, domin mu magance wannan matsala baki daya a yankunanmu, gwamnati ba ta da zabin da ya wuce daukar matakan da suka hada da bai wa mutane damar mallakar bindigogi domin kare kansu daga ‘yan bindiga.

Gwamnati ta umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya bai wa dukkan mutanen da suka dace kuma suke bukatar mallakar bindiga su mallake ta domin kare kansu.

Labarai Makamanta