Zamfara: Matawalle Ya Nada Sabbin Hadimai 250

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle na Jihar ya kara nada sabbin masu rike da mukaman siyasa a jihar don taimakawa wurin gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Darakta Janar na Harkokin Siyasa da Alaka Tsakanin Jam’iyyu, Alhaji Mikailu Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Gusau, ranar Laraba.

Aliyu ya ce dalilin nada sabbin hadiman shine don tabbatar da ganin romon dimokradiyya ta kai ga mutane a kauyuka da karkara. Ya ce tun bayan kafa gwamnatin, gwamnan ya nada kwamishinoni 25, mashawarta na musamman 55, Manyan direktoci 72 da mambobin kwamitin amintattu 12.

Ya ce wadanda aka yi wa nadin mukaman siyasan 250 sun hada da manyan daraktoci guda takwas, manyan mashawarta na musamman 242 hakan ya kawo jimillar masu mukaman siyasa a jihar zuwa 1,700.

Aliyu Mikailu ya kuma yi watsi da zargin da ake yi na cewa gwamnatin jihar tana bibiyan wani Shamsu Shehu, Shugaban Marafa Social Media, yana mai cewa zargin baya da tushe. Ya ce gwamnatin Matawalle mai son zaman lafiya ne kuma tana bawa kowa ‘yancin tofa albarkacin bakinsa da shiga duk jam’iyyar da ya ke so a jihar.

Labarai Makamanta