Zamfara: Matawalle Ya Kirkiro Sabbin Ma’aikatu

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan jihar Bello Matawalle ya tabbatar da samar da ma’aikatu 4 sannan ya zabo sababbin kwamishinoni na ma’aikatun.

Ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya bayyana a Gusau ranar Litinin.

A cewar Balarabe, ma’aikatun da ya kafa guda 4 su ne: 1-Ma’aikatar kula da dazuka da bunkasa kiwon dabobbi. 2- Ma’aikatar samar da dukiya da kuma samar da ayyuka. 3-Ma’aikatar yawon bude ido da kula da otal. 4-Ma’aikatar gina gidaje da bunkasa birane.

Balarabe ya bayyana yadda gwamnatin ta nada sababbin kwamishinoni wadanda za su fara aiki daga nadin. Ya lissafo ma’aikatun da kwamishinonin kamar haka;

1-Ahmed Anka – Ma’aikatar ilimin kimiyya da fasaha. 2-Abubakar Dambo – Ma’aikatar harkokin kananun hukumomi. 3-Muh’d Magaji – Ma’aikatar al’adu. 4-Nasiru Masama – Ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni. 5-Abdulaziz Nahuce – Ma’aikatar ayyuka na musamman. 6-Zainab Gummi – Ma’aikatar ilimi. 7-Sufyan Yuguda – Ma’aikatar kudi 8-Fa’eka Marshal – Ma’aikatar harkokin jin kai da annoba. 9-Rabiu Gusau – Ma’aikatar ayyuka da tafiye-tafiye. 10- Yazeed Fulani – Ma’aikatar sana’o’i da ma’aikatu. 11-Ibrahim Gusau – Ma’aikatar dazuka da bunkasa kiwon dabbobi. 12-Nuradden Gusau – Ma’aikatar ma’adanai. 13-Junaidu Kaira – Ma’aikatar shari’a 14- Mai Akwai Ibrahim Magayaki – Ma’aikatar noma. 15-Ibrahim Dosara – Ma’aikatar labarai. 16-Yahaya Gora – Ma’aikatar ilimin gaba da sakandare . 17-Yahaya Kanoma – Ma’aikatar samar da ayyuka da bunkasa arziki. 18-Lawal Badarawa – Ma’aikatar bunkasa al’umma. 19-Sheikh Jangebe – Ma’aikatar harkokin addini. 20-Aliyu Tukur – Ma’aikatar kasafi da tsare-Tsare. 21-Aliyu Tsafe – Ma’aikatar lafiya. 22-Mamman Tsafe – Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida. 23-Abubakar Tsafe – Ma’aikatar yawon bude ido da kula da otal. 24-Ibrahim Mayana – Ma’aikatar ruwa. 25-Abubakar Bore – Ma’aikatar bunkasa kauyaku.

Labarai Makamanta