Zamfara: Matawalle Ya Bada Umarnin Buɗe Makarantun Kwana

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar mai girma Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Bello Matawallen Maradun ya bada umarnin sake buɗe dukkanin Makarantun kwana dake jihar, bayan rufe su da aka yi tsawon lokaci sakamakon fitinar ‘yan Bindiga.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle, ya ce an yanke wannan shawara ne domin dalibai su samu komawa karatu, domin fuskantar kalubale na Ilimi dake tafe.

Gwamnan ya kuma gargadi jami’an makarantun kan amsan kudade daga hannun iyayen yara inda ya bayyana fushin sa akan haka da kuma alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace.

Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta ɗauki matakin rufe makarantun kwana a jihar ne tun bayan wani hari da ‘yan Bindiga suka kai a makarantar sakandaren kwana ta gwamnati dake Jangeɓe ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a kwanakin baya suka yi awon gaba da ‘yan mata masu yawa.

Daga bisani an yi nasarar ceto ‘yan matan waɗanda suka kai kusan 300 bayan shafe kwanaki cikin dokar daji da ‘yan Bindigar, inda aka karɓe su a fadar gwamnatin jihar dake Gusau.

Mai girma Shugaban ƙasa Buhari ya nuna tsananin damuwa da baƙin cikin sa akan satar daliban, inda ya bayyana cewar wannan satar daliban ita ce ta ƙarshe ba za’a kuma ba.

Sai dai an samu akasi, bayan furucin Shugaban ƙasar an cigaba da kai hare hare a makarantu ana satar ɗalibai, harin baya bayan nan shine wanda ‘yan Bindiga suka kai a makarantar koyon dabarun noma da gandun daji dake Kaduna suka yi awon gama da dalibai masu yawa.

Labarai Makamanta