Zamfara: Manyan Kwamandojin ‘Yan Bindiga Sun Shiga Hannu

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Haukumar tsaro (NSCDC), ranar Laraba, ta sanar da kame wasu tsagerun yan bindiga guda huɗu akan iyakar Jihar Zamfara da jihar Sokoto.

An ruwaito cewa waɗanda ake zargin ‘ya’yan manyan ƙungiyoyin yan bindiga ne da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara, Kaduna da Jihar Katsina.

An yi nasarar damke mutanen ne bisa zargin hannu a garkuwa da manyan mutane, fashi da makami, satar dabbobi da kuma kashe mutane a wasu yankunan waɗannan jihohi.

Kwamandan jami’an NSCDC reshen jihar Sokoto, Mohammed Saleh-Dada, yace wasu daga cikin mutanen da aka damke yan leken asirin yan bindiga ne. A cewar kwamandan hukumarsu ta gayyaci wani babban mutum da ake zargin yana da alaƙa da ɗaya daga cikin mutanen da aka kame.

“Mun gayyaci wani sanannen mutum a yankin karamar hukumar Dange/Shuni, jihar Sokoto, bisa zargin yana da wata alaƙa da mutum daya da ake zargi.”

Labarai Makamanta