Zamfara: Madugun ‘Yan Bindiga Ya Yi Tuban Muzuru

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Shahararren dan bindigan nan da ya jagoranci satan daliban Kankara 300, Auwalu Daudawa, ya koma daji bayan kimanin watanni uku da alanta tubarsa daga kisan kai da satar mutane.

An ruwaito cewa wata majiyar jami’an tsaro da wasu majiyoyi na kusa da ɗan bindigan sun tabbatar da cewa Auwalu Daudawa ya koma dajin dake da iyaka da jihar Katsina.

Auwalu Daudawa ne ya jagoranci satan daliban makarantar GSS Kankara ranar 12 ga Disamba, 2020. Bayan watanni biyu da hakan , gwamnan jihar Zamfara ya sanar da cewa Daudawa ya tuba daga garkuwa da mutane kuma ya ajiye makamansa.

Daudawa da yaransa biyar sun mika bindigogin AK47 guda 20, harsasai barkatai, da roka 1 a wancan lokacin. Majiyoyi sun bayyana cewa Daudawa ya kwashe yaransa sun koma dajin Jaja, dake karamar hukumar Zurmi ranar Litinin.

“Ya kira daya daga cikin mutanensa a Gusau domin sanar da shi cewa ya isa dajin kuma ya yanke shawaran komawa harkar. Bai fadawa kowa kafin tafiyarsa ba,” daya daga cikin majiyoyin ya fada.

An ce Daudawa ya fusata ne saboda rashin cika alkawuran gwamnati bayan ajiye makamansa. Gwamnati ta ba Daudawa da yaransa wajen zama na tsawon makwanni kafin aka saya masa gida a Damba, domin zamansa da iyalinsa.

Labarai Makamanta