Zamfara: Kotu Ta Haramtawa Majalisa Tsige Mataimakin Gwamna


Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar wata Babbar Kotu dake birnin tarayya Abuja ta dakatar da majalisar dokokin jihar Zamfara daga daukar matakin tsige mataimakin gwamna jihar, Mahdi Aliyu daga kan mukaminsa.

Jam’iyyar PDP ce ta shigar da ƙarar, bayan wata ƙarar da ta kai gaban kotun ƙolin Najeriya, tana neman fashin baki a kan makomar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da mafi yawan ƴan majalisar dokokin jihar da na tarayya, wadanda suka sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

An shiga takun saka a tsakanin Gwamnan jihar Bello Matawalle da mataimakin nashi Mahadi Aliyu Gusau tun bayan sauya sheka da gwamnan ya yi daga Jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Hukuncin kotun zai zama wata nasara ce ga jam’iyyar PDP da Mahadi Aliyu Gusau mataimakin gwamna, wanda ke hanƙoron ganin ya dare karagar mulkin jihar.

Labarai Makamanta