Zamfara: Kotu Ce Kawai Za Ta Rabani Da Mai Mala Buni – Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, yayi watsi da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC a jihar wanda aka baiwa alhakin juya akalar jam’iyyar a jihar.

Shugabannin jam’iyyar na kasa ne suka kafa kwamitin rikon kwaryan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ya rushe zababbun shugabannin jam’iyyar na jihar kafin sauya shekar Gwamna Bello Matawalle.

Kafin wannan cigaban, Yari ne shugaban jam’iyyar a jihar Zamfara. Bayan rikicin da sauya shekar Matawalle ke tafe da shi, Buni ya kafa kwamitin rikon kwarya na mutum 3.

Amma Yari wanda ya caccaki Buni, ya ce bai aminta da kwamitin ba.

A wata tattaunawa da yayi da BBC, ya ce rushe shugabancin jam’iyyar a jihar Zamfara bai dace ba.

Tsohon gwamnan ya ce Buni bashi da ikon rushe shugabancin jam’iyyar dake karkashin ikonsa, inda yace hakan zai iya janyo wani rikici a jam’iyyar.

Ya kara da cewa, shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar da aka nada yanzu ba asalin ‘ya’yan jam’iyya bane.

Daya daga cikin hakkin kwamitin rikon kwaryan shine samar da yanayi da dukkan mambobin jam’iyya zasu sabunta rijistarsu.

Amma Yari yana barazanar daukar matakin shari’a inda yace an nada kwamitin rikon kwaryan ne yayin da aka yi karantsaye ga kundun tsarin mulkin jam’iyyar.

Labarai Makamanta