Zamfara: Gwamnati Ta Biya Diyyar ‘Yan Sanda 7 Da Aka Kashe

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta baiwa iyalan jami’an yan sanda bakwai da yan bindiga suka kashe a jihar kudi Naira Miliyan Bakwai.

A baya kun ji yadda yan bindiga suka kaiwa jami’an yan sanda harin kwantan bauna a hanyar Tofa-Magami, ranar 8 ga Nuwamba, 2021.

Kwamishanan yan sandan jihar, Ayuba Elkana, ya baiwa iyalan kowanne cikin kudi milyan guda-guda madadin gwamnatin jihar, domin saukaka musu radadin rashin da suka yi.

Elkana yace gwamnatin ta basu kudin ne don rage radadi da halin da suka shiga sakamakon rashin mazajensu. Ya yi bayanin cewa jami’an yan sanda sun sadaukar da kawunansu don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A cewarsa, yan sandan da abin ya shafa sune Jonah Markus, Solomon Abiri, Stephen Ishaya, Nura Ibrahim, Abdul Garba, Musa Lawal da Zubairu Sadiq.

Labarai Makamanta