Zamfara: Ba ‘Yan Bindigar Dana Gani Bane Suka Sace ‘Yan Mata – Gumi

Malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya ce ba yan bindigan da ya gana da su a dajin Zamfara bane suka sace yan matan makaranta a jihar. The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun afka makarantan Gwamnati na Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara misalin karfe daya na daren Alhamis inda suka sace dalibai mata fiye da 300.

”Kwamishinan tsaro da harkokin gida na Zamfara, Alhaji Abubakar Dauran ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai, NAN, sace yan matan amma bai tabbatar da adadin wadanda aka sace din ba. Gumi, cikin gajeren hirar wayar tarho da jaridar The Nation, ya ce wasu kungiyar daban ne suka sace yan matan a Zamfara amma ba wanda ya gana da su ba. Malamin addinin musuluncin wanda ya gana shugabanin yan bindigan a Zamfara ya ce ya tuntube su kuma sun ce, “Ba su ne suka sace yan matan makarantar ba, wata kungiyar ne daban.” Da aka masa tambaya ko zai tafi Zamfara domin ganawa da yan bindigan don a sako yan matan, Sheikh Gumi ya amsa da cewa, “wata kila”.

Malamin ya tafi dazukan Zamfara domin yi wa yan bindigan nasiha sannan ya yi ji kokensu inda ya yi kira ga gwamnati ta duba yiwuwar yi musu afuwa. Gumi da tawagarsa sun kuma gana da wasu yan bindigan a dazukan Sububu da Pakai.

Kuna ganin sulhu da yan bindiga shine kadai mafita a halin da kasar mu ke ciki na shakakin tsaro?

Labarai Makamanta