Zamfara: An Zakulo ‘Yan Majalisar Dake Harka Da ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Majalisar jihar ta dakatar da mambobinta biyu da ta zarga suna da alaƙa da ƴan bindiga masu fashi da satar mutane.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na majalisar Zamfara Mustapha Jafaru Kaura ya fitar a ranar Talata ta ce an dakatar da ƴan majalisar ne na tsawon wata uku zuwa lokacin da aka kammala bncike kan zargin da ake masu.

Ya ce za su gurfana gaban kwamitin ɗa’a da na tsaro waɗanda za su yi bincike a kansu.

Yan majalisar biyu da aka dakatar su ne Yusuf Muhammad Anka da ke wakiltar karamar hukumar Anka da kuma Tukur Bakura dan majalisa da ke wakiltar Bakura.

Sai dai ƴan majalisar biyu da ake zargi ba su cikin zauren majalisar lokacin da aka zartar da matakin da kuma zargin da ake masu.

Ɗaya daga cikin ƴan majalisar da ake zargi Yusuf Muhammad Anka ya mayar da martani inda ya shaida wa BBC cewa “bita da ƙullin siyasa ce kawai, saboda mun yi yunkurin tsige kakakin majalisa.”

Wasu bayanai daga majalisar sun ce majalisar ta ɗauki matakin ne saboda yunkurin da ɗaya daga cikin ƴan majalisar da ake zargi yake na sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, watanni bayan ya koma jam’iyyar APC tare da gwamnan jihar da kuma sauran ƴan majalisar.

Ɗan majalisa Yusuf Alhassan Kanoma da ke wakiltar Maru ta arewa ne ya gabatar da kudirin, “kuma bayan yin muhawara, majalisa ta amince da kudirin dakatar da ƴan majalisar guda biyu.”

Majalisar ta zargi mambobin guda biyu da ta dakatar da yin murna lokacin da aka sace mahaifin shugaban majalisar Hon Nasiru Mu’azu Magarya wanda rahotanni suka ce ya mutu a hannun ƴan bindiga.

“Mun ji cewa Yusuf Muhammad Anka and Ibrahim T Tukur Bakura suna ta yin murna kan batun.”

“Suna da hannu da kisan ɗaya daga cikin ƴan majalisar da ke wakiltar shinkafi ta hanyar yin waya da ƴan bindiga wanda ya kai ga kashe shi,” in ji sanarwar.

Majalisar kuma ta ba jami’an tsaro umarni su saurari maganganunsu a wayoyinsu na salula daga cikin hanyoyin binciken tabbatar da zargin da ake masu.

Short presentational grey line

Umarnin na zuwa bayan gwamnatin jihar Zamfara ta tilastawa sabbin kwamishinoni da sakatarorin gwamnati yin rantsuwa da Al Kur’ani cewa ba su da hannu da ƴan bindiga.

Gwamnan jihar kuma ya fito yana ƙalubalantar dukkanin shugabannin siyasar musamman masu hamayya da shi su fito su yi rantsuwar cewa ba su da hannu da matsalar tsaron jihar, kamar yadda ya rantse da jami’an gwamnatinsa

Labarai Makamanta