Zamfara: An Yanke Shawarar Sulhu Da Shugaban ‘Yan Bindiga Turji

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Sakamakon hare-haren wuce gona da iri a yankin Shinkafi a jihar Zamfara, musamman kan matafiya dake kan hanyar da ta hada Gusau zuwa Sabon Birni, a jihar Sokoto, an aika da sabon jakada domin ganawa da kasurgumin dan bindiga, Turji.

A farkon watan Nuwamba, Turji ya yi watsi da tawagar Shinkafi ta neman tattaunawa, wadanda rahotanni suka ce sun je wurinsa domin neman zaman lafiya, duba da yadda kashe kashe suka kazamce a yankin.

Wani mazaunin garin Shinkafi, Alhaji Ali Mamman, ya ce an sha kai hare-hare a babbar hanyar tun bayan harin da sojoji suka kai ta sama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar iyaye da sauran ‘yan uwa na aminin Turji, Dan Bokkolo.

A baya an ruwaito yadda sojoji suka yi ruwan bama-bamai a maboyar ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma. An shafe kwanaki ana kai hare-haren, inda wani mazaunin garin ya shaida cewa ‘yan bindigar na kai hare-hare a wasu lokutan har sau uku a kullum.

Ya ce duk da haka mazauna yankin sun sami kwanciyar hankali bayan tura karin sojoji a ranar Litinin.

An gano cewa tawagar ta bar garin Shinkafi ne da yammacin ranar Litinin din da ta gabata don ganawar. Sai dai ba a san sakamako ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Labarai Makamanta