Zamfara: An Gudanar Da Zanga-Zanga Da Gawawwakin Mutane

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Zanga-zanga ta barke a safiyar ranar Juma’a a garin Zurmi, hedkwatar karamar hukumar Zurmi saboda yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da ke kashe mutane a garuruwa kamar Kaji a kullum.

An ruwaito cewa Mutane da dama sun rasa rayyukansu wasu daruruwan sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren yan bindiga da ya ki-ci ya-ki-cinyewa a garuruwan jihar.

A makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kai hari a wani gari a karamar hukumar Zurmi inda suka kashe fiye da mutane 11. Mazauna garin sun shaidawa majiyarmu cewa garuruwa da dama a yankin na fuskantar barazana daga yan bindiga.

Masu Zanga-Zangar sun dauko tarin wasu gawarwakin sun shiga gari suna zanga-zanga nuna damuwarsu kan hare-haren da yan bindiga ke kai musu. Wani daga cikin mazauna garin da ya ce sunansa Mustapha ya ce: “Suna hanyarsu zuwa fadar sarki domin gabatar da kokensu.

“Sai dai, Sarkin bai fito ya gana da su ba domin an ce yana can cikin gida. Sun yi kone-kone kafin suka tafi. “Masu zanga-zangan sun bar fadar sunnan suka hadu a hanyar Gusau zuwa Jibia suka fara tare Motocin matafiya da ke bin titin.

“Sun kuma fasa gilasan motoccin da aka ajiye a gefen titi.” “Yanzu abubuwa sun dai-daita a yayin da jami’an tsaro ke sintiri a titunan garin domin tabbatar da doka da oda. “Sannan mutane sun koma sun cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba,” in ji shi.

An yi kokari ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu amma ba a same shi ba a yayin hada wannan rahoton.

Labarai Makamanta