Zamfara: An Damƙe Sojan Dake Taimakon ‘Yan Bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar a ranar Juma’a cewa an kama wani soja shi da budurwar sa su na kai wa masu garkuwa makamai da kakin soja a cikin jihar.

Mataimakin Gwamnan Zamfara, Bashir Maru ne ya bayyana haka, a wani taro da manema labarai da ya yi, inda ya wakilci gwamna Bello Matawalle.

Maru ya ce sojoji ne da kan su su ka kama sojan ta hanyar wasu kauyawa mazauna yankin da su ka labarta wa sojoji aika-aikar da sojan ke kan yi.

Sai dai kuma ya bayyana cewa ba zai yi wani karin bayani ba, ya na jira hukumomin sojojin Najeriya su yi sanarwar irin aiak-aikar da sojan ke yi kafin a kama shi.

“Ba a dade ba sjoji sun damke wani soja shi da budurwar sa su na kai wa masu garkuwa da mutane makamai da kuma kayan sojoji. Wannan kuma laifin zagon-kasa ne.

“Yayin da gwamnatin jihar Zamfara ke jiran hukumar sojoji ta dauki mataki kuma ta fito ta yi karin bayani, to wannan lamari ya tabbatar da gaskiyar da Gwamnan Zamfara da ya ce idan har ba kakkabe baragurbi da musu yi wa shirin samar da tsaro kafar-ungulu ba, to ba za a taba yin wata nasara a yaki da ‘yan bindiga ba.

“Ina so na yi amfani da wannan dama ta hanyar kafofin yada labaran kuma na yi godiya da jinjina ga mutumin da ya sadaukar da kan sa har ya bayar da labarin da ya kai ga damke wadannan maciya amana.” Inji Mataimakin Gwamnan Zamfara.

Dama Gwamna Matawalle ya sha fada cewa akwai masu yi wa shirin samar da tsaro zagon-kasa a Zamfara.

Ko cikin makon nan ya bayyana cewa sace daliban Jangebe kulle-kullen siyasa ne.

Matawalle ya bayyana cewa da mai gadin sakandaren Jangebe aka hada baki aka sace daliban mata.

Ya kara da cewa lokacin da masu garkuwa su ka sallami daliban, sun ce idan sun koma makaranta, su gaida mai gadin, wanda su ka ambaci sunan sa, tare da cewa ba su san akwai wata makarantar mata a Jangebe ba, sai da shi mai gadin ya sanar da su.

Sannan kuma Gwamnan ya yi ikirarin cewa a lokacin da ake kokarin sakin daliban Jangebe, wasu marasa kishi kuma marasa imani na dankara wa ‘yan bindiga kudade don kada su saki daliban.

Labarai Makamanta