Zamfara: An Cafke Jakadiyar Shugaban ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan sanda a jihar sun cafke wata mai shekaru 30, mai suna Fatima Lawali dauke da harsashi na bindigar AK-47 har guda 991, akan hanyarta ta shiga dokar daji wurin ‘yan bindiga.

Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba Elkanah, yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma’a ya bayyana hakan, ya ce wacce ake zargin tana kan hanya ne zuwa kai wa wani hatsabibin dan bindiga mai suna Ado Alero, wanda ya dade yana adabar mutanen Zamfara da kewaye Harsasai.

Kwamishinan yan sandan ya ce: “A ranar 25 ga wannan watan da muke ciki misalin karfe 0930hrs, yan sandan rundunarsa da na FIB/STS karkashin jagorancin DSP Hussaini Gimba sun kama wata mata mai suna Fatima Lawali, yar asalin karamar hukumar Kauran Namoda wacce ta kware wurin yi wa yan bindiga safarar makamai a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina da Niger.”

An kama ta a Gada Biyu da ke karamar hukumar Bagudu dauke da harsashi dari tara da casa’in da daya (991) na bindigar AK-47 za ta kai wa shugaban yan bindiga mai suna Ado Alero a kauyen Dabagi a jihar Sokoto.

Labarai Makamanta