Zaman Lafiyar Najeriya Shine Afuwa Da Daukar Nauyin ‘Yan Bindiga – Gumi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shahararren malamin addinin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ƙara jaddada matsayarsa cewa yi wa yan bindiga afuwa da ɗaukar nauyin su ne kaɗai hanyar kawo ƙarshen zubar da jinin mutane a Arewa.

Malamin ya yi wannan furuci ne a wurin sanya marayu rukuni na uku a shirin samar musu da ilimi, kula da lafiya kyauta, wanda gidauniyar musulunci a Kawo ta ɗauki nauyin shiryawa.

Sheikh Gumi ya shawarci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari, kada ta zama silar ƙarin kashe-kashen mutane, ta hanyar kuskuren da take kokarin yi na ayyana ‘yan Bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Malam Gumi yace: “Idan har akwai wata hanya da zata dakatar da zubar da jini, zai fi kyautuwa a yi musu kwatankwacin abinda aka yi wa mayaƙan Niger Delta.” “Sun kasance suna fasa bututun mai da zubar jinanen mutane, amma aka yi musu afuwa suka aje makamansu idan za’a musu afuwa da ɗaukar nauyinsu, inaga za’a iya yi wa yan bindiga haka.”

“Mun gana da su kuma a shirye suke su aje makamansu. Amma idan sun daina kuma ba’a samar musu da ilimi ba, da kuɗin da zasu kula da kansu, zasu koma gidan jiya ne.”

Labarai Makamanta