Zaman Lafiya Da Lumana Zai Dawo Najeriya – Fadar Shugaban Kasa

An bayyana cewar ko shakka babu zaman lafiya da lumana na kusa da dawowa Najeriya bayan tsananin wahalar da kasar ta fuskanta tsawon lokaci, inda aka buƙaci ‘yan Najeriya da ka da su yanke tsammanin faruwar hakan.

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yana mai cewa “akwai alkawarin Allah” ga Najeriya kuma kasar za ta zama “gidan zaman lafiya, tsaro da ci gaba irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a wannan nahiya da ma ta gaba da ita.”

Ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake jawabi a wajen babban taron shekara-shekara karo na 108 na Babban Taron Baptist na Najeriya a garin Abeakuta babban birnin Jihar Ogun.

Farfesa Osinbajo ya kara da cewa Najeriya “za ta kasance cibiyar ci gaban tattalin arziki da kimiyya na karni na 21,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa Laolu Akande ya sanya hannu akai.

Mataimakin Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, ba mai iya ja da lamarin Allah ko wane ne shi inda yake cewa: “Ina da cikakken yakinin cewa babu wani, babu wata kungiya, ko wata akida, da za ta iya karya alkawarin Allah don cigaban Najeriya.”

Sai dai, ya lura cewa “a yau gizagizai sun lullube, alkawarin kamar ba zai yiwu ya cika ba, kamar yadda ya kasance ga ‘ya’yan Isra’ila bayan barinsu Misira kan hanyar su zuwa kasar da aka alkawarta musu.”

Kalaman na Mataimakin Shugaban na zuwa ne yayin da kasar ke ci gaba da fama da kalubalen tsaro da dama. Kasar na fuskantar matsaloli kamar tayar da kayar baya a Arewa-maso-Gabas, ‘yan ta’adda a yankin Arewa-maso-Yamma, da tayar da zaune tsaye a Kudu-maso-Gabas da rikicin Fulani-makiyaya a duk yankin na Tsakiyar Arewaci da kuma jihohin Kudu maso Yamma da dama.

Labarai Makamanta