Zaman Lafiya A Afirka: Buhari Zai Halarci Taro Yau A Kasar Murtaniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari a ranar yau Litinin zai yi tafiya zuwa Nouakchott, babbar birnin jamhuriyyar ƙasar Mauritania domin halartan taron shugabannin kasashen Afrika kan zaman lafiya.

Wannan shine karo na uku da wannan taro zai gudana. Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a wajen taron kan nasarorin da aka samu wajen samar da zaman lafiya a Afrika.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce a wajen taron za’a baiwa Shugaba Buhari kyautar lambar yabon “Mai Karfafa Zaman Lafiya A Afrika”. A cewarsa, za’a bashi wannan lambar yabo ne bisa jagorancin da ya nuna wajen wanzar da zaman lafiya a nahiyar ta hanyar gudunmuwa da sulhun da ya taimaka da shi.

Femi Adesina ya ce cibiyar zaman lafiyan Abu Dhabi ce zata gabatar da wannan lambar yabo.

“Gabanin bashi lambar yabon tabbatar da zaman lafiya a Afrika, Shugaban kasa zai halarci taron zaman lafiyan Afrika karo na uku inda zai gabatar da jawabi kan nasarorin da aka samu wajen samar da zaman lafiya a Afrika.”

“Shugaban kasan zai tafi Nouakchott ranar Litinin sannan ya dawo ranar Laraba kuma zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; ministan tsaro, Maj. Gen. Bashir Salihi Magashi; NSA Babagana Munguno da Dirakta janar na NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.”

Labarai Makamanta