Zakzaky Makaryaci Ne – Hukumar DSS

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ranar Litinin, ta zargi shugaban kungiyar IMN, wacce aka fi sani da Shi’a, Ibrahim Zakzaky, da kirkirar karya ya jingina mata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa hukumar ta musanta zargin da shehin malamin ya yi cewa ta karkatar da wasu kuɗaɗe da aka tura masa da matarsa yayin da suke tsare.

A wata hira da jaridar Punch, Malam Zakzaky, ya zargi DSS da wawure kudin alawus ɗinsu na wata-wata miliyan N4m yayin da suke tsare.

Ya kuma zargi cewa hukumar DSS ta yi amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen kula da abincin jami’anta da kuma wasu kayayyaki na tsawon lokacin.

Amma kakakin DSS, Dakta Peter Afunanya, yace maganar malamin zuƙi ta malle ce da ya shirya domin bata wa hukumar suna. Afunanya yace: “Wannan tsagwaron ƙarya ce da aka shirya domin cutar da hukumar tsaro kamar DSS.

Abun takaici ne mutum kamar shi (Zakzaky) ya zabi yin ƙarya. Da yuwuwar ya rasa basirar banbance gaskiya da ƙarya.” “DSS ba ta zaluntar waɗanda ake zargi. Yayin da ya tafi Indiya a shekarun baya, shi da kansa ya nemi ya dawo hannun jami’an DSS. Meyasa? saboda yana samun kulawa mai kyau a cewarsa.”

“Idan mutum yasan yana da kalubale a kotu, zai fi masa kyau ya maida hankali kan abin da ke damunsa, kuma a daina zargin DSS.” DSS na mutunta doka Afunanya ya ƙara da cewa a kowane lokaci hukumar DSS na bin dokoki kuma tana samun jagoranci bisa doka da tsari.

Labarai Makamanta