Zaben Najeriya: Ba Ma Goyon Bayan Kowa Cikin ‘Yan Takara – Birtaniya

Wakiliyar Birtaniya a Nijeriya, Catriona Liang, ce ta bayyana hakan a yau Laraba bayan wata ganawar sirri da ta yi da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa, NWC, a Abuja.

Liang ta yi nuni da cewa, UK za ta yi aiki da duk wani dan takarar da ya lashe zaɓe, inda ta bayyana amincewa da dimokuradiyyar Nijeriya da kuma kudurin shugaban kasar na yin zaɓe cikin kwanciyar hankali kuma ingantacce.

Ta ce: “Wannan taro ɗaya ne da na ke yi da jam’iyyun siyasa, da ƴan takarar shugaban kasa, da kuma shugabannin jam’iyyar. Kuma a yau ne shugaban jam’iyyar APC ya isar da sakon mu game da babban zabe.

“Muna maraba da kudurin Nijeriya na tabbatar da dimokuradiyya da kuma kudurin shugaban kasa na tabbatar da zabe mai inganci.

“Mun yi magana kaɗan dalla-dalla game da yanayin da ya dace don hakan ya faru. Da kuma damuwa game da rashin tsaro.

“Sannan kuma muhimmancin fitowar jama’a a wannan rana da kuma karfafa wa mutane da dama yin rajista domin su na bukatar fitowa zaɓe a ranar zabe.

“Hakan yana nufin babu razanar wa sannan a sanar da ingantaccen muhalli. Kuma mutane su ji cewa za su iya zaben dan takarar da su ke so.

“Birtaniya ba ta da wani ɗan takara da ta ke goyon baya. Mun himmatu wajen gudanar da sahihin zabe, amma za mu yi aiki da duk wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben.

“Birtaniya da Nijeriya su na da kawance mai karfi, kuma muna son Nijeriya ta yi nasara. Kuma dimokuradiyya ɓangaren nasarar ce,” in ji ta.

Labarai Makamanta