Zaben Ekiti: Manuniya Ce Ta Nasarar APC A 2023 – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhamadu Buhari, ya yi wa zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Ekiti a ƙarƙashin Jam’iyyar APC murnar lashe zaɓen gwamnan jihar.

A wani saƙon da Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya buƙaci duka Ƴan Jam’iyar APC a ciki da wajen Najeriya da su kalli wannan zaɓen a matsayin manuniyar nasarar APC a zaɓen 2023.

Shugaba Buhari ya yaba wa Biodun Oyebanji kan nasarar da ya samu a zaɓen inda ya ce ya cancanci ya zama gwamna sakamakon irin gudunmawar da ya bayar wurin kawo ci gaba a Jihar Ekiti da kuma Jam’iyyar APC a jihar tun kafin ya zama ɗan takara.

A ranar Asabar ne dai aka gudanar da zaɓen Jihar Ekiti inda Biodun Oyebanji ya lashe zaɓen da ƙuri’a 187,057.

Labarai Makamanta