Zaben Anambra: Wankin Hula Ya Kai INEC Dare

Rahotanni daga Jihar Anambra na bayyana cewar har kawo ya zuwa yanzu ana cigaba da tattara sakamakon zaben Gwamna da ya gudana a ranar jiya Asabar.

Wani mai sanya ido na hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ya shaida wa BBC cewa ya ga wakilan jam’iyyu daban-daban a rumfunan zaɓe na siyan kuri’ar jama’a a wasu yankunan jihar, da suka haɗar da karamar hukumar Dunukofia, da Anaocha, da Awka, da Njikoka da Aguata.

Jami’in ya ce ”Jama’a kin fitowa suka yi sai wajen ƙarfe huɗu na yamma, saboda an fara fito da kuɗi, an fitar da kudi sosai, kowacce jam’iyya ma ta siya, su kansu wakilan jam’iyyun sun rinka sasantawa a tsakaninsu, idan wakilin wata jam’iyya a wata rumfa ya ga baza su kai labari ba sai ya sasanta da wanda yake da rinjaye a wannan wajen.”

Ya ƙara da cewa ”Ni da idona na ga ana siyar da ƙuri’a a kan Naira dubu uku, wasu wuraren naira dubu biyar, su jami’an tsaro saboda sun ga zaɓen na gudana cikin lumana sai suka mayar da hankalinsu zuwa tsakiyar jihar, ya kasance wasu wuraren ma idan ka je baza ka tarar da ko jami’in ɗan sanda daya ba.

Jami’in ya ƙara da cewa zaɓen ya gudana cikin lumana, don duk rumfar kaɗa ƙuri’ar da ka je za ka taras da mutane suna annushuwa suna farin ciki babu wata alamar fargaba, saboda kwanciyar hankalin da aka samu

”Tun da nake halartar zaɓe ban taba ganin inda aka jibge jami’an tsaro kamar wannan ba, shi yasa ma ƴan ƙungiyar IPOB suka janye matakin da suka ɗauka na hana zaɓen, domin sun lura cewa idan ma suka yi wani yunƙuri ba za su kai labari ba” inji shi

To sai dai ya ce ”An samu matsala da na’urorin zaɓe, a wurare da yawa bayan an shirya an kammala komai ga kayan zaɓe amma na’urori suka ki tantance masu jefa ƙuri’a sai wajen yamma aka fara”.

A halin da ake ciki dai ana jiran ganin wanda zai lashe zaɓen, wanda yan takara goma sha takwas daga jam’iyyu daban-daban suka fafata.

Labarai Makamanta