Charles Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA ya lashe zaɓen ƙananan hukumomi goma sha ɗaya kawo yanzu da ake cigaba tattara ƙuri’un da aka kaɗa.
Ƙananan hukumomin sun haɗa da Awka South, Onitsha South, Orumba South, Anaocha, Anambara East, Njikoka, Orumba North, Aguwata, Oyi, Ayamelum, da Dunukofia.
Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta sanar da cewa za a cigaba da tattara sakamakon zaɓen gobe Lahadi.
Akwai ƙananan hukumomi 21 a jihar Anambra, amma sakamakon 11 kaɗai aka sanar.
Kawo yanzu, Charles Soludo na da jimillar ƙuri’u 74,859 daga ƙananan hukumomin 11, yayin da ɗan takaran PDP, Valentine Ozigbo na PDP ke biye da shi da ƙuri’u 30,581 sannan Andy Uba na APC mai ƙuri’u 26,056.
Ga jerin sakamakon:
Njikoka LGA:
APC – 3,216
APGA – 8,803
PDP – 3,409
YPP – 924
Awka South:
APC – 2595
APGA – 12891
PDP – 5489
Onitsha South LG:
APC – 2050
APGA – 4281
PDP – 2253
Orumba South:
APC: 2,060
APGA: 4,394
PDP: 1,672
YPP: 887
Anambra East LGA:
APC 2034
APGA: 9746
PDP: 1380
Anaocha LGA:
APC – 2085
APGA – 6911
PDP – 5,108
Orumba North:
APC – 2692
APGA – 4826
PDP – 1863
Aguwata:
APC – 4773
APGA – 9136
DP – 3798
Dunukofia:
APC – 1991
APGA -4124
PDP – 1680
Oyi:
APC – 2830
APGA – 6133
PDP – 2484
Ayamelum:
APC – 2409
APGA – 3424
PDP – 2804
You must log in to post a comment.