Zaben Anambra Bai Kammalu Ba – INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana zaben Gwamnan Jihar Anambra a matsayin wanda bai kammala ba.

Farfesa Florence Obi, jami’ar da ke kula da zaben ne ta bayyana hakan a babban ofishin Hukumar INEC da ke Awka, babban birnin Jihar Anambra, da daren ranar Lahadi.

Ta ce zaben ba zai iya kammaluwa ba a tashin farko saboda ba’a gudanar da za’be a karamar hukumar Ihiala da ke jihar ba.

A dalilin haka ne ta ce za’a gudanar da za’be a karamar Hukumar ta Ihiala ranar Talata mai zuwa, kamar yadda dokar za’be ta tanadar.

Labarai Makamanta