Zaben Abuja: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Jaddada Dokar Hana Zirga-Zirga

Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta bada sanarwar tsaurara matakan hana zirga-zirga a daidai lokacin da ake gudanar da zabukan kananan hukumomi a birnin.

Sanarwar da rundunar ta fitar ya bayyana cewar za a hana dukkanin wata zirga-zirga a birnin tun daga misalin karfe takwas na safe har zuwa karfe uku na rana domin samun gudanar da zabukan kananan hukumomi a yankin a ranar yau Asabar.

Rundunar ta ƙara da cewa ɗaukar matakin hakan ya biyo bayan rahoton da suka samu ne dake nuna cewa wasu bata gari na da wani shiri na yin kutse kan dukiyoyin jama’a a daidai lokacin da ake harkar zaɓe.

Sanarwar wacce take dauke da sanya hannun Kwamishinan ‘yan Sanda Babaji Sunday ta tabbatar da samar da tsaro ga jama’ar birnin a daidai lokacin da zaɓukan ke gudana.

A baya dai rundunar ta sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga a birnin kafin daga bisani ta janye wannan sanarwar bayan samun rahotannin tsaro.

Labarai Makamanta