Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce ana ta samun yunƙurin kutse ga tsarin kwamfutocinmu lokacin da muke fuskantar zaben 2023.
Yakubu ya bayyana haka a ranar alhamis yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja, wanda aka yi wa take “Zaɓen 2023″ shari’a tare da tabbatar da dimokradiyya mai dorewa”.
Shugaban wanda mataimakin daraktan kula da fasahar zamani Dr Lawrence Bayode ya ce hare-haren da ake fuskanta ana samunsu ne daga sassa daban-daban na duniya ba iya Najeriya ba.
“Muna cikin duba kwamfutocinmu jiya, sai kawai muka ga wasu mutane daga Faransa na neman yi mana kutse, amma nan take muka ɗauki mataki.
You must log in to post a comment.