Zaben 2023: Gwamnonin Kudu Sun Yi Taron Gaggawa

‘Ya’yan ƙungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma sun gana a jihar Legas domin tattaunawa a kan batun babban zabe dake tafe da kuma lamarin tsaro.

Gwamnonin sun tattauna muhimman batutuwa wanda suka shafi matsalolin yankinsu, da kuma hanyar kawo cigaba. Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, shine ya karbi bakuncin takwarorinsa a gidan gwamnati, kwanaki uku kacal bayan harin da aka gidan yari a Ibadan. Gwamnoni biyar sun samu halartar taron, wanda aka fara shi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma kuma cikin sirri.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, shine bai samu halarta ba, amma ya turo mataimakinsa, Rauf Olaniyan, ya wakilce sa.

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, yace sun tattauna batutuwa da dama. Gwamnan ya bayyana cewa a wani ɓangaren tattaunawar tasu sun yi mahawara kan yanayin tsaron da suke fama da shi a yankin.

Labarai Makamanta