Shugaban kungiyar ‘yan Shi’a ta IMN a Najeriya, Ibrahim Zakzaky ya yi watsi da rahotannin da ke ikrarin yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a zaben dake na wannan shekara ta 2023.
A baya wasu kafafen yaɗa labarai sun yada rahoton da ke bayyana cewa, shugaban na ‘yan Shi’a ya bi sahun tsohon shugaban kasa Obasanjo da kuma shugaban Neja Delta Edwin Clark wajen marawa Peter Obi baya.
Hakazalika, rahoton da ya yadu a kafafen sada zumunta ance ya yi kira ga ‘yan Shi’a miliyan takwas dake Najeriya da su tabbatar da mallakar katin zabe, kuma su zabi Peter Obi a zaben shugaban kasa.
Sai dai, daya daga cikin lauyoyin malamin, Marshall Abubakar na Falana & Falana Chambers, ya ce wannan labarin na karya ne, don haka Zakzaky bai bayyana marawa Peter Obi baya ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng! A cewarsa:
“Wancan labarin karya ne. Zan iya tabbatar muku cewa babu wani abu mai kama da wannan. “Duk da cewa wasu ‘yan takarar shugaban kasa sun gana dashi, ya nisanci marawa daya daga cikinsu baya saboda ya yi imani zaben 2023 na shugaban kasa batu ne da ke da alaka da fahimta.”
You must log in to post a comment.