Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi gwamnatocin ƙasashen ketare kan tsoma baki ko katsalanda a harkokin cikin gidan ƙasar musamman a lokutan zaɓe da ke tafe kasa da kwanaki 42.
Shugaban ya sanar da hakan ne lokacin da yake maraba da sabbin jakadun Switzerland da Sweden da Jamhuriyar Ireland da Thailand da Senegal da Sudan ta Kudu a fadar gwamnati.
Shugaban ya ce Najeriya tana aiki kafada-kafada da kungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas domin shawo kan matsalolin tsaro da bijiro da matakan tabbatar da zaɓe mai sahihanci ba tare da katsalanda ga kudin tsarin mulkin kasa ba.
Ko a shekarar da ta gabata sai dai shugaba Buhari ya yi irin wannan gargadi inda yake cewa burinsa shi ne ganin anyi sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta rawaito shugaba Buharin ya gargadin jakadun ketare kan su mayar da hankali kan abin da ya shafesu da dalilan turo su Najeriya, da kuma kawar da kai kan abubuwan da ba huruminsu ba ne.
Buhari ya ce babu shaka dole za a sa ido kan yada zaɓukan Najeriya za su kasance don haka fatansa shi ne ganin wakilan ƙasashen sun mayar da hankali wajen shirya yada ayyukansu zai kasance domin tabbatar da ganin komai ya tafi cikin kwanciyar hankali.
Sannan ya shaida mu su cewa Najeriya tana aiki sosai da Ecowas domin tabbatar da cewa an mututun dokokin kudin tsarin mulki ba wai kowa damar ‘yanci zaɓen abin da yake so.
Ya kuma jadada cewa yana alfahari da farin ciki irin haɗin-kan da ƙasashen ke bai wa Najeriya musamman a fanonin da suka shafi tsaro da yaƙi da rashawa da inganta tattalin arziki da kuma kokarin haɓɓaka shugabanci na gari.
Ya nemi hadin-kan sauran kasashen duniya wajen shawo kan manyan kalubalen Najeriya da yammacin Afirka.
You must log in to post a comment.