Zaben 2023: Ba Za Mu Amince A Sake Yaudarar Mu Ba – Sheikh Jingir

Shugaban majaisar malamai na ƙungiyar Izala reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, yace ba zasu sake yarda yan siyasa su s yaudare su ba, kamar yadda aka yaudare su a baya.

Sheikh Jingir ya yi wannan furuci ne yayin da yake wa’azi a wurin wa’azin ƙasa da ƙungiyar ta saba shiryawa, wanda ya gudana a Jingir jihar Filato.

“Kada mu sake mu yarda wani ɗan siyasa ya je ya siyar da kuri’un mu da sunan yarjejeniyar tsarin mulkin karba-karba a babban zaɓen 2023.” “Wannan tsarin da yan siyasa ke magana a kansa tamkar wata caca ce, kuma yana nufin wasu tsirarun mutane yan siyasa sun maida yan ƙasa tamkar kayan su.”

Mu mallakin Allah ne, Jingir ya kara da cewa mutane ba bayin yan siyasa bane da zasu juya su yadda suka ga dama, mutane bayin ubangiji Allah ne. “Kuri’un mu na hannun mu kuma mu zamu zaɓi wanda muke so idan muka ga ya dace kuma yana da manufofi masu kyau.”

“Don haka kada mu sake wasu su maida kuri’un mu marasa amfani, har wani ya samu ikon zuwa bada yawun mu ba, ya bada kuri’un mu.”

Sheikh Yahaya Jingir ya yi kira ga yan Najeriya baki ɗaya su fita kwansu da kwarkwata su zabi mutanen kirki a babban zaɓen 2023 dake tafe. A cewarsa akwai bukatar yan Najeriya su kula wajen tantance wanda zasu zaɓa, kada su zaɓi waɗanda zasu mance da al’ummar su.

Labarai Makamanta