Za Mu Zakulo Gami Da Hukunta Masu Haddasa Fitina A Najeriya – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa za a ci gaba da kokarin zakulo masu son haddasa fitinan kasar dake addabar mutane, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne bayan kammala Sallar Idin Layya a gidansa da ke Daura a jihar Katsina, a ranar Talata.

Duk da cewa bai bayar da misali ko ambatar sunan wani ba, amma kalaman nasa na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da aka kama mai fafutukar kafa kasar Yarabawan nan Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday Igboho.

Hukumar yan sanda Ta kasa da kasa (Interpol) ce ta kama Mista Igboho a Cotonou babban birnin Jamhuriyyar Benin.

Labarai Makamanta