Za Mu Yi Wa Kasa Dabaibayi Muddin ASUU Ba Ta Janye Yajin Aiki Ba – Dalibai

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar reshen ɗalibai na Gamayyar Ƙungiyoyin Farar hula na Arewa, CNG-SW sun yi barazanar rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ƙasa da manyan titunan Arewa in har gwamnatin tarayya da ASUU ba su sansata an janye yakin aikin da suke yi ba.

Ɗaliban sun kuma yi barazanar rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewacin Nijeriya.

Ƙungiyar ta yi wannan barazana ne a wata takardar bayanin bayan taro, wanda Kodinetocin kungiyar na jihohi 19 su ka gudanar ranar Juma’a a Kano.

Da ya ke karanta takardar ga manema labarai, Kodinetan kungiyar na ƙasa, Jamilu Charanchi ya ce Ƙungiyar ta cika da damuwa bisa yadda yajin aikin ASUU da na kwalejojin ilimi ya ci tura.

A cewar ƙungiyar yajin aikin ya jefa ƴaƴan talakawa cikin wata irin mawuyaciyar rayuwa.

Kungiyar ta ƙara da cewa tuni ta ɗauki gabaran rubuta ƙorafi ga Sarakunan gargajiya, malaman addini, jami’an gwamnati da jami’an tsaro a kan su saka baki a kawo karshen yakin aikin.

“Idan haka ba ta samu ba, to za mu rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ƙasa da manyan titunan Arewacin Nijeriya.

“Za kuma mu rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewa,” in ji su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply