Za Mu Yi Amfani Da Salon Katsina Wajen Ceto Ɗaliban Neja

Ministan tsaron Najeriya Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, ya bayyana cewa hukumar Sojoji za ta yi amfani da dabarar da akayi amfani da ita wajen ceto daliban Kankara domin ceto daliban makarantar gwamnati dake Kagara, a jihar Neja.

Bashir Magashi, ya bayyana hakan ne yayin zantawar shi da manema labarai a zauren majalisar wakilan tarayya ranar Talata yayinda ake tantance sabbin hafsoshin tsaron da shugaba Buhari ya nada.

Ministan ya ce hafsoshin tsaron za su bazama aiki ana kammala tantancesu. Yace: “Mun nuna bajintarmu wajen dakile irin wannan matsalan. Mun yi a Katsina; lokacin da aka sace yara, muka dawo dasu cikin kwanaki biyu.

Muna kyautata zaton cewa yanzu ma haka zamuyi domin dawo da su. Muna shiri.” “Bamu samu bayanan abubuwan dake faruwa a jihar Neja ba har yanzu, amma ina da tabbacin cewa kafin rana ta fadi, zamu samu cikakken labarin halin da ake ciki a jihar Neja.”

A wani labarin na daban Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma’aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata 16 ga watan Fabrairu.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

Mun kuma ji cewa, babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Mohammed Babagana Monguno, Shugaban ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, sun halarci garin Minna, babban birnin jihar Neja. Sauran tawagar sune ministan labarai, Lai Mohammed da takwaransa na harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, domin tattauna yadda za’a samu mafita wajen ceto ɗaliban.

Labarai Makamanta