Za Mu Yaƙi Ta’addanci Iyakar Ƙarfin Mu – Gwamnoni

Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya 36 karkashin shugabancin jagoranta, gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, ta bayyana alhini da kuma murna ga gwamnatin jihar Zamfara da al’ummar jihar, game da samun nasarar kubutar da ‘yan matan nan da aka sace daga makarantar kwana ta garin Jangebe.

A lokacin da yake bayyana matakin da kungiyar gwamnonin ta dauka, na ganin ta tashi tsaye don kawo karshen irin wannan mugun aikin, gwamnan ya ce zasu bada duk taimakon da ake bukata don ganin irin wannan mugun aikin bai samu waje a kasarba.

Ya kara da cewar, sun ware wani abu da zasu bai wa gwamnatin Zamfara a matsayin ta su gudunmawa, don ta iya magance wannan matsalar da ta yi kamari a jihar.

Gwamnan ya yi na’am da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na kafa dokar ta baci a jihar ta Zamfara. A lokacin na shi jawabin, gwamnan jihar Zamfara Alh. Bello Matawallen Maradun, ya bayyana godiyarsu ga Allah, saboda samun nasarar maido da wadannan yaran gida cikin koshin lafiya.

Ya kuma kara da cewar, yanzu ba lokaci bane na dora laifi ga wani ko wata ba, lokaci ne na tashi tsaye don kawo karshen wannan matsalar, a waje daya kuma ya tabbatar cewar bukatar shi a jihar, ita ce, al’ummah su iya bacci da idanuwansu biyu a rufe, koda kuwa ta kai ya bar kujerar ta shi.

Labarai Makamanta