Za Mu Tura ‘Yan Sanda 10,000 Da Aka Yaye Aiki Lokacin Babban Zabe – Baturen ‘Yan Sanda

Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya sanar da cewa, sabbin kwasitabul din ‘yan sanda da aka yaye kwanakin nan, da suka kai 10,000 za a ba za u a sassan kasar ldomin tabbatar da doka da oda lokacin zaben shekarar 2023 da ke tafe.

Jaridar intanet ta Solacebase, ta ambato mataimakin sufeton ‘yan sandan shiyya ta 8, Ashafa Adekunle, wanda ya wakilci babban sufeton ‘yan sandan Najeriyar, IGP Usman Alkali Baba, na bayyana haka a wurin bikin yaye daliban makarantar horon ‘yan sandan da ke Ilori.

”Mu na shaida muku bayan faretin kammala horas da sabbin ‘yan sanda, za a baza su a sassan Najeriya lokacin zabukan da ke tafe na shekarar 2023. Za su yi aikin tabbatar da tsaro domin a gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da luma,” in ji Adekunle.

Ya yin da babban zaben Najeriyar ke kara karatowa, ana nuna damuwa kan sha’anin tsaro da ke kara tabarbarewa a wasu sassan kasar musamman arewacin Najeriya da ake fama da barayin daji da masu satar mutane domin kudin fansa.

Labarai Makamanta