Za Mu Tura Sabbin Kuratan Sojin Da Aka Ɗauka Dajin Sambisa – Buratai

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa Hukumar Sojojin Najeriya za ta yi tankade da rairaye da zazzage a daukar kuratan sojoji, ta yadda sai wadanda su ka cancanta kadai za a dauka aiki.

Ya ce babu wani gurbi ko guda daya da za a dauki wanda bai cancanta ba a jefa cikin aikin soja.

Laftanar Janar Buratai dai ya yi wannan ban-tsoron a lokacin da ya ke jawabi wajen tantanace kuratan sojoji a Dajin Falgore, cikin Jihar Kano a ranar Litinin.

Ya ce wannan aikin tantance sabbin dauka na kuratan sojoji wani sabon salo ne aka shigo da shi.

Ya ce an shigo da sabon salon ne a bisa bukatar da ake da ita ta daukar sabbin kuratan sojoji a kasar nan.

Ya kara da cewa darussan da aka dauka a baya ya sa tilas a yanzu aka fito da sabon salon daukar kuratan sojoji.

Ya kara da cewa, “daukar wadanda ba su cancanta ba ke sa ana samun aikata abin da bai cancanta ba wajen gudanar da ayyukan harkar tsaron kasa.”

Buratai ya ce Hukumar Sojojin Najeriya ba za ta kara kara daukar wadanda ba su cancanta ba.

” Matsawar dai ku ka yi amanna a zukatan ku cewa kun amince za ku yi wa kasar ku ta haihuwa aiki, a matsayin ku na sojoji. To sai ku shirya amincewa da duk inda za a tura ku bayan kun kammala samun horo.

“Kowanen ku sai an tura shi Dajin Sambisa, bayan kun kare tirenin a daffo.” Inji Buratai.

” Duk wanda bai shirya ma shiga Dajin Sambisa ba ko duk ma wani wuri da kan iyakokin Najeriya domin kare kasar sa ba, to ya sani bai ma fara aikin ba kawai.

“Duk wanda ya san bai shirya wa yin aiki ba kuma bai shirya wa bin na gaba da yin da’a ba, to bai makara ba, zai iya mikewa ya tafi gida abin sa kawai.

“A aikin soja ba a son ragwanci, ba a son rashin da’a, kuma ba a son lusaranci.” Inji Buratai.

Ya ce daga yanzu tantancewa, horaswa da dauka duk a Dajin Falgore za a rika yi.

Wadanda aka tara a Dajin Falgore dai su 6,000 ne, kuma daga jihohi 36 aka dauko su, inda ake ba su horo na dauka aikin soja.

A karshe dai za a zuba su kan titi domin yin gudun tsawon kilomita 10. Daga nan za a dauke su zuwa Makarantar Horas da Kananan Sojoji ta Zari’a.

Labarai Makamanta

Leave a Reply