Za Mu Tsamar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 35 Daga Talauci Nan Da Shekaru Uku – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sufuri na Alhaji Muazu Sambo ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da ayyukan yi kusan miliyan 21, tare da cire mutum miliyan 35 daga talauci nan da shekarar 2025.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan ya fitar, ya ce ministan ya fadi hakan ne ranar Juma’a a taron ministocin da ke gudana a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Ministan ya ce ma’aikatar sufurin kasar za ta shirya wasu matakai domin cimma wannan mataki.

”Za mu zuba jari mai yawa a fannin abubuwan more rayuwar jama’a, da tabbatar da daidaituwar fannin tattalin arziki, da bunkasa hanyoyin zuba jari, da kuma aiwatar da matakan magance dumamar yanayi”, inji Ministan.

Ya kara da cewa ”hakan zai samar da ayyukan yi kusan miliyan 21 tare da fitar da mutum miliyan 35 daga talauci nan da shekarar 2025, da wannan mataki za mu cimma kudurin gwamnatin tarayya na fitar da mutum miliyan 100 daga talauci nan da shekara 10.

Bincike ya nuna cewa miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da matsanancin talauci da ba a gani ba a shekaru 15 da suka gabata, lamarin da ake ɗora alhakin hakan akan gwamnatin Buhari.

Sai da a martanin da gwamnatin tarayya ke bayarwa dangane da wannan zargin tana bayyana cewar ƙasar ta tsinci kanta ne a halin da take ciki sakamakon bullar cutar Korona da kuma karyewar farashin mai a kasuwannin duniya.

Labarai Makamanta