Za Mu Tabbatar PDP Ta Yi Nasara A Jihohin Mu – Gwamnonin G5

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya yi magana da zai iya bawa Atiku Abubakar kwarin gwiwa da jam’iyyar PDP. Ortom, a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, ya ce shi da takwarorinsa a PDP na G5 ba za su yi watsi da jam’iyyarsu ba, za su tabbatar ta yi nasara a Jihohin su.

Gwamna Samuel Ortom ya ce karkashin jam’iyyar PDP aka zabi gwamnonin na G5 kuma har yanzu su yan jam’iyya na masu kishinta. Gwamnan na Benue ya yi wannan jawabin ne bayan kaddamar da yakin zaben tazarcen Gwamna Seyi Makinde a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

A wata sanarwar da babban sakataren watsa labaransa, Nathaniel Ikyur, ya fitar, Ortom ya ce gwamnonin na G5 za su yi aiki tukuru don ganin PDP ta yi nasara a jihohinsu a babban zaben da ke tafe.

Labarai Makamanta