Za Mu Samar Da Cibiyoyin Kiran Gaggawa Na Waya A Fadin Najeriya – Pantami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami, ya bayyana shirinsa na samar da aƙalla cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) ɗaya a kowace jiha kafin ƙarewar 2022,

Ministan ya faɗi haka ne a wajen ƙaddamar da sabon tsarin tattalin arziƙin zamani rukuni na 10 a babban birnin tarayya Abuja.

A cewar Pantami, an ƙaddamar da ECC 23 a faɗin Najeriya, kuma akwai ragowar 13 da ake cikin aikin su. Rahoton BBC ya nuna cewa tuni ministan ya buɗe ofishin farko a wannan tsarin a jihar Katsina matakin da ya bai wa sama da mutum 40 aikin yi.

“A cikin shekaru biyu, mun buɗe sabbin Cibiyoyin amsa kiran gaggawa 23 a faɗin Najeriya, kuma kawai sauran 13 dake tafe.” “Tsarin da muka yi shine a samar da aƙalla ECC ɗaya a kowacce jiha dake faɗin Najeriya kafin ƙarshen shekarar 2022.”

“Waɗannan cibiyoyin suna da matuƙar amfani, Lamba ce da zakai amfani ita kyauta, idan ka kira lambar ba za’a caje ka ko sisi ba.”

Pantami ya kara da cewa wannan tsarin zai taimaka wa yan Najeriya wajen bada haɗin kai da taimaka musu wajen isar da saƙon gaggawa musamman akan tsaro.

Labarai Makamanta