Za Mu Rushe Gidajen Masu Ba ‘Yan Ta’adda Bayanan Sirri – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi alkawarin rushe gidajen masu bai wa yan fashin daji bayanai ko kuma suke samar musu da makamai a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin da yake karbar bakuncin gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal da yan majalisarsa da suka kai masa ziyarar jajantawa ga gwamnati da al’ummar Zamfara game da hare-haren baya-bayan nan da aka kai a wasu sassan jihar.

Matawalle ya ce ya umarci a dauki tsauraran matakai har da rushe gidajen duk wani da aka samu mai bai wa yan fashin daji bayanai ne da kuma kama wadanda suke taimaka wa yan bindigar wajen kai hare-hare ba tare da bata lokaci ba.

Cikin sanarwar da Yusuf Idris Gusau, daraktan yada labarai na gwamnan Zamfara ya fitar, matakin ya zamo dole domin a kawo karshen karuwar hare-haren yan fashin daji a wasu sassan jihar da yadda wasu yan cikin jihar ke ba da gudummawa wajen ruruwar matsalar.

Matawalle ya bayyana cewa karuwar hare-haren na haifar da koma-baya a yakin da ake inda ya bukaci jama’a a jihar su ba da gudummawa wajen ganin an murkushe yan fashin dajin.

Labarai Makamanta