Za Mu Magance Matsalar Sabbin Kudi Nan Da Mako Guda – Buhari


Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci ƴan ƙasar da su ba shi kwanaki bakwai kacal domin shawo kan matsalolin kuɗi da suke kawai tasgaro a ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani taro da ya yi da ƙungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC waɗanda suka je fadar shugaban ƙasar domin neman mafita kan ƙarancin kuɗin da ake fama da shi waɗanda suka ce hakan na barazana kan ayyukan alkhairi da gwamnatin ta yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya ce sauya fasalin kuɗin da aka yi zai haɓaka tattalin arzikin ƙasar da kuma samar da tagomashi na tsawon lokaci ga ƙasar.

Haka kuma shugaban ya nuna damuwa kan lamuran wasu bankuna a ƙasar inda ya ce kansu kaɗai suka sani kuma a cewarsa ko shekara guda aka ƙara, matsalolin da suke tattare da san kai da zari ba za su gushe ba.

Hakan bai rasa nasaba da kalaman da gwamna El Rufai ya yi a wata hira da BBC inda ya ce akwai wani gwamna daga cikin gwamnonin ƙasar da ya samu sabbin kuɗi har naira miliyan 500.

Labarai Makamanta

Leave a Reply