Za Mu Koyar Da Matasa Dubu 30,000 Ilimin Fasahar Zamani – Pantami

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace za’a horad da karin matasan Najeriya sama da 30,000 ilimin fasahar zamani.

An ruwaito cewa wannan na ɗaya daga cikin amfanar da yan Najeriya za su yi da hadin guiwar ma’aikatar sadarwa da kamfanin Huawei Technologies Nigeria.

Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) tsakanin ɓangarorin biyu, da nufin ƙara inganta ilimin zamani (Digital Literacy) ga yan Najeriya.

Kazalika kamfanin ya yi amfani da taron wajen mika kyaututtuka ga waɗanda suka samu nasara a zango na karshe a gasar Huawei.

“Yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta sa wa hannu ta ma’aikatar sadarwa, a ɗaya hannun kuma kamfanin Huawei Nigeria, zai maida hankali ne wajen kara inganta kwarewar yan Najeriya.”

“Musamman saboda yadda duniya ke canza wa a yanzu, akwai bukatar dalibai su samu kwarewar fasaha da za su iya yin abu a aikace . “Shiyasa mukai tunanin samar da MoU domin ganin, a ɓangaren kokarin da kamfanin Huawei ke yi, sun tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan.”

Labarai Makamanta