Za Mu Kashe Daliban Da Suka Saura Idan An Gaza Biyan Miliyan 100 A Yau – ‘Yan Bindigar Kaduna

A hira da gogarman masu garkuwa da mutane yayi da wakilin Tashar Amurka ta ayar tarho, Sani Jalingo, wanda ake kira da ‘Baleri’ ya bayyana cewa wannan gargado da yake yi shine na karshe, itan gwamnati bata ji ba, zai kashe daliban gaba dayan su sai da a zo a kwashi gawarwakin su a manyan motoci.

Baleri ya ce iyayen yaran sun biya baira miliyan 55 amma kuma da wannan kudi ne suka rika ciyar da daliban garin kwaki.

” Iyayen yaran sun aiko mana da miliyan 55, amma kuma hakan bai ishe mu ba domin wadannan kudi ma abinci muka siya wa daliban makarantan.

” Wannan karin shine na karshe da za mu yi kira da akawo wadannan kudade. Idan har ya ki rabar Talata ba a biya ba, tabbas sai xai kuma iyaye su hakura da yayan su domin sai dai kuma gawar su.

” A kawo mana naira miliyan 100 da sabbin babura kirar Honda guda 10. Babu wani abu da muke bukata bayan haka. Idan aka aiko da kudin zamu saki sauran yara, idan ko aka ki to sai gawarsu daga rabat Talata.

Baleri ya ce shi ba mummunar abu yake yi ba, saba ace ya ce yi domin samun abinci.

Wasu daga cikin daliban, da suka yi magana da VOA sun bayyana cewa lallai fa abin da Baleri ke fadi ba kuri ko ba a bane, lallai za su aikata abin da su me cewa.

” Muna rokon gwamnati da iyayen mu su yi Allah su zo su biya wadannan kudade mu koma gidajen mudomin idan ba su biya wadannan kudade ba za su kashe mu.

Daya daga ciki daliban da aka kama, jikan marigayi sarkin Zazzau Shehu Idris ne.

Labarai Makamanta