Za Mu Hukunta Duk Bafillacen Da Aka Samu Da Aikata Laifi – Buhari

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya nesanta kansa daga aika-aikar wasu Fulani a cikin Najeriya.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa Shugaba Buhari ya ce ba ya goyon bayan garkuwa da mutane da hallaka jama’a tare da barnar da wasu Fulani ke yi a cikin Nijeriya.

A daidai lokacin da shugaba Buhari ke wannan jawabin, ya umarci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Karkashin Shugaban `Yan Sandan IGP Adamu Muhammad Abubakar da ya bayyana Sunayen Fulanin da ake shari’a da su a kotu Akan Zargin Su Da Aikata laifin garkuwa da mutane kwashe dukiyar al’umma tare da allaka jam’a a cikin Nijeriya domin gaggauta Zartar Masu da hukunci mai tsuri a cikin Nijeriya.

Majiyar Mu Ta sanar Mana Da Cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wannan umarnin ne a jiya Litinin. Inda yake cewa lallai ya zama dole Gwamnatin Shi ta hukunta duk wani wanda aka kama da laifin cin amanar tsaron Nijeriya.

Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan sandan Nijeriya su fito da sunayen duk Fulanin da ake zargi da laifi domin tabbatar da cewa hukunci ya hau kan shi.

Shugaban ya umarci jami’an ‘yan sanda da su wallafa sunayen gaba daya makiyaya Fulanin da ake shari’a da su a kotu da zargin aikata laifuffuka.

Kamar yadda majiyar mu ta Labarta mana cewa, shugaban kasar ya bada wannan umarni ne domin nuna babu hannunsa a wajen wanke makiyaya Fulani a cikin Nijeriya.

Masu karatu idan kun tuna ana zargin Shugaba Buhari da yi wa ta’adin Fulani rufa-rufa saboda kabilarsu daya.

Mai ba shugaban kasar shawara wajen yada labarai, Garba Shehu ne ya bayyana wannan a lokacin da aka yi hira da shi a shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels TV.

Garba Shehu Ya ce Shugaba Buhari ya damu iya damu wa a kan halin da ake ciki, ya na sane cewa nauyin gwamnati ne ta tsare rayukan al’umma Sannan Kuma ta kawo karshen rikicin da ake yi, daga garkuwa da mutane zuwa sababbin laifuffukan da ake yi na fadan kabilanci.

Muna Rokon Ubangiji Allah Ya Zaunar Mana Da Kasar Mu Najeriya Da.

Labarai Makamanta